Home Labarai Amnesty ta magantu kan simamen jami’an tsaro shelkwatar NLC

Amnesty ta magantu kan simamen jami’an tsaro shelkwatar NLC

Kungiyar kare haƙƙin bil’Adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadarai da samamen da jami’an tsaro suka kai hedikwatar ƙungiyar kwadago ta Najeriya, ta NLC.

Kungiyar ta ce samamen da aka kai jiya Laraba da daddare ya yi kama da wata mummunar manufa ta hantarar ƙungiyar ƙwadagon.

A cewar Amnesty International, samamen da jami’an tsaron suka kai ya tauye ƴanci da damar ma’aikata na gudanar da zanga-zanga.

A yayin samamen, jami’an tsaron sun yi awon gaba da littattafai na kungiyar NLC, tare da kwace kayayyakin da suka ce an yi amfani da su wajen tada zaune tsaye da kuma shirya zanga-zangar baya-bayan nan.

Ƙungiyar ta Amnesty ta bayyana matukar damuwarta game da tsaron jami’an NLC.

Sannan ta jaddada cewa a karkashin dokokin kare hakkin bil’Adama na ƙasashen duniya, ba a harin ƙungiyoyin ƙwadago saboda gudanar da ayyukansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp