Shugaban Comoros, Azali Assoumani ya ɗan ji rauni bayan da wani ya kai masa farmaki da wuƙa a jiya Juma’a, kamar yadda kakakin gwamnatin ƙasar ta bayyana, tana mai cewa an kama maharin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 agogon GMT a Salimani Itsandra wani gari da ke arewacin babban birnin ƙasar, Moroni, inda shugaban ya je ta’aziyar rasuwar wani babban malamin addinin Islama na ƙasar, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana wa kamfanin dilancin labarai na Reuters.
Kakakin gwamnatin, Fatima Ahamada ta ce shugaba Assoumani ba ya cikin haɗari sakamakon raunin, kuma tuni ya koma gida.
Ganau sun ce maharin wani matashi ne mai shekaru 22, wanda ba shi da tarihin aikata laifi, kuma ya shiga aikin soja a shekarar 2022.
Wuƙar ta ji wa shugaban rauni, amma wani daga cikin mutanen da ke zaman makoki ya kama maharin.
PRNigeria Hausa










