Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.1 daga bankin raya Afirka (AfDB) don samar da wutar lantarki ga mutane miliyan 5 daga yanzu zuwa ƙarshen shekarar 2026.
A cewar Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan a cikin jawabin da Adebayo Adelabu, ministan wutar lantarki, ya gabatar, a taron da aka kammala na kwanaki biyu na inganta ɓangaren makamashi na Afirka a Dar es. Salaam, babban birnin ƙasar Tanzania.
Tinubu ya kuma bayyana cewa za a yi amfani da dala miliyan 200 na AfDB domin samar da wutar lantarki ga mutane 500,000 a ƙarshen shekarar 2025.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Wannan babban buri ne, amma za mu iya cimma shi tare,” in ji Tinubu.
“A matsayina na shugaban Najeriya, na himmatu wajen ba aiwatar da aikin samar da makamashi, kuma mun ba da babban fifiko.”
Ya ƙara da cewa “Kamar yadda muka sani, Afirka na da wadatar albarkatun makamashi, amma har yanzu miliyoyin ƴan nahiyar mu ba sa samun ingantaccen makamashi mai araha.”
Shugaba Tinubu kuma jinjinawa Ajay Banga, shugaban bankin duniya, da Akinwunmi Adesina na AfDB saboda hangen nesan su na kawo sauyi, wanda ya ce “zai haskaka da kuma karfafa Afirka.”











