Rahotanni daga jihar Filato na bayyana cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun hallaka mutum biyar a karamar hukumar Bokkos na jihar.
Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi da daddare na zuwa ne kwanaki 11 bayan kai hari makamancinsa a karamar hukumar tare da kashe mutum bakwai.
an ruwaito cewa shugaban ƙungiyar ci gaban al’ummar Bokkos, Farmasum Fuddang, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma yin Alla-wadai da shi.
Read Also:
- Ƴan Sandan Legas Sun Kama Mutum 4 da Ake Zargi da Fashin Daji, Sun Kwato Wayoyin Hannu 25, Kwamfutoci da Kayan Ado na Zinare
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Rusa Wuraren Tace Mai Ba bisa Ka’ida Ba, Ta Kwato Lita 350 na AGO a Rivers
- 2027: Yahaya Bello Ya Tara Masu Daidaita Ayyuka na A4A a Arewa ta Tsakiya Domin sake Zaban Tinubu
Ya ce an yi mutanen da aka kashen kwantan ɓauna lokacin da suke balaguro daga garin Mbar zuwa kauyen Koh na jihar.
Ƴan bindigar sun je ne a kan babura inda suka yi wa garin dirar mikiya da misalin karfe 7 na yammaci.
Fuddang ya soki jami’an tsaro saboda rashin mayar da martani a kan lokaci, inda ya ce kafin zuwarsu maharan sun riga da sun tsere.
Ya kuma nuna damuwar cewa irin waɗannan hare-hare da ake kai wa za su iya ɗaiɗaita al’ummomin yankin gabaki ɗaya.
PRNigeria Hausa










