Hukumar da ke yaki da yi wa masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya EFCC ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, bayan ta yi masa tambayoyi kan wawushe dukiyar ƙasa da ya kai sama da Naira biliyan 189.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
An gayyaci Tambuwal wanda ya mulki jihar Sokoto daga shekarar 2015 zuwa 2023, zuwa hedikwatar EFCC da ke Abuja ranar Litinin, inda ya isa da misalin karfe 11:30 na safe.
Masu bincike sun yi masa tambayoyi kuma daga baya aka tsare shi a shelkwatar hukumar.
Majajiyoyi sun ce, a ranar Talata, aka saki tsohon gwamnan bayan cika sharuddan belinsa, waɗanda aka bayyana a matsayin mara tsauri.
Ƴan adawa sun bayyana tsare tsohon gwamnan da EFCC ta yi, a matsayin wani yunƙuri na karya lagon ƴan adawa da gwamnati maici a ƙasar ke yi.











