Home General Mazauna Djibo a Burkina Faso sun buƙaci cikakkiyar kariya daga ƴan ta’adda

Mazauna Djibo a Burkina Faso sun buƙaci cikakkiyar kariya daga ƴan ta’adda

Mazauna garin Djibo na lardin Soum a Burkina Faso sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi don neman a inganta musu tsaro biyo bayan mummunan harin ta’adanci da aka kai garin.

Mata, maza da yara ne suka  bazama kan titunan garin  a matsayin martani ga kutsen da ƴan bindiga suka yi a gari  amakon da ya gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 3, waɗanda ƴan ta’addan suka yi wa yankan rago.

Ɗaya  daga cikin masu zanga-zangar da ya bayyana dalilin fitowar su cikin  fushi ta cikin wani hoton bidiyo, ya ce ƴan ta’addan su na yi musu kutse cikin birnin, inda su ke kashe iyaye, matansu da ƴaƴansu.

Dubban mutane ne suka arce daga wasu sassan birnin da ɗan kayayyakin da za su iya ɗibawa, biyo bayan wa’adin da  wata ƙungiyar ƴan ta’adda ta ɗibar musu.

Hotunan da aka wallafa a shafukan dandalin sada zumunta sun nuna ɗimbim mutane a ruɗe su na barin birnin a ƙasa da jakuna.

Wasu mazauna birnin sun ce ƙungiyar ƴan ta’addan ta bai wa al’ummar  su koma yankuna  na 7,8 da 9 na Djibo. Amma waɗannan yankuna sun kasance a ƙarƙashin ikonsu tsawon shekara guda, amma a maimakon haka sai su ka nufi sansanin soji kai tsaye a cewar majiyoyi da dama.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp