‘Yan Daba Sun Farmaki Kasuwar Sayar da Wayoyin Hannu a Jihar Kano
Kano, Nigeria – Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari fitacciyar kasuwar sayar da wayoyin hannu watau Farm Center da ke cikin kwaryar birnin jihar Kano.
Rahotanni da ba a tabbatar da su ba, sun nuna cewa wasu daga cikin maharan sun fito ne daga wani taron siyasa da aka gudanar , sai dai babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da hakan.
Matakin da jami’an tsaro suka dauka
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Daga bisani, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin, inda suka tarwatsa maharan tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasuwar ta Farm Center.
Wata majiya a kasuwar ta shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa, ana zargin ƴan daban sun halarci wani taron siyasa da aka yi a yankin, kafin su farmaki wajen siyar da wayar da ke Yoyo Plaza.
Majiyar ta kara da cewa, ƴan daban sun daka wawa tare da kai sara ga ƴan kasuwar dake tsaka da ciniki, haka kuma, sun dinga kwacewa mutane wayoyinsu a kan hanya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu tabbacin mutuwar kowa, amma an ce mutane da dama sun samu raunuka Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba tukuna, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.












