Home Taska Ƙungiyar MURIC na Zargin Gwamnatin Najeriya da Nuna wa Musulmai Bambanci

Ƙungiyar MURIC na Zargin Gwamnatin Najeriya da Nuna wa Musulmai Bambanci

Tinubu MURIC

Ƙungiyar MURIC na Zargin Gwamnatin Najeriya da Nuna wa Musulmai Bambanci

 

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta zargi gwamnatin Najeriya da nuna fifiko tsakanin Musulmai da Kiristoci a ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan da rahotanni suka ce gwamnatin tare da ƙungiyar Kiristoci (CAN), sun ƙaddamar gina wani katafaren coci da za kashe wa naira biliyan 25 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

A wata sanarwa da MURIC ta aike wa BBC, shugaban ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya kuma nuna takaici kan yadda gwamnatin ta tallafa wa waɗanda rikici ya shafa a jihar Filato da naira biliyan 2, ba tare da ta yi irin hakan a jihohin Sakkwato, Borno, Kebbi da Zamfara ba, da su ma suke fama da matsalolin tsaro.

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayanin dalilin da ya sa ake nuna wannan fifiko. Musulmai a Najeriya ba su cancanci haka ba…,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin Najeriyar ta ware irin waɗannan kuɗaɗe na kimanin naira biliyan 25, da kuma fili ga Musulman ƙasar domin su ma su gina katafaren masallaci a filin jirgin.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Wannan haƙƙin mu ne. Kuma ya kamata a ba mu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp