Gwamnan Bauchi ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar APM
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APM.
Gwamnan ya sanar da matakin ne a fadar gwamnatin jihar a yau asabar, inda shugaban APM ya karɓe shi tare da ba shi katin shiga jam’iyyar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Rahotanni sun ce ya fice ne tare da wasu mambobin jam’iyyar PDP masu goyon bayan shugabancin Tanimu Turaki.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki da gwamnan na jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi.
Dama dai a hirarsa da BBC, gwamnan ya ce, tun bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan rikicin PDP ya ƙuduri aniyar ficewa daga jam’iyyar.
Kafin sauya sheƙar tasa, shi ne shugaban gwamnonin jam’iyar PDP












