Home Taska Gwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram

Gwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram

Mai Mala Buni

Gwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram

Gwamnatin Yobe ta yi alƙawarin sake tumke ɗamarar kawo ƙarshen sabbin hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram da haramtaccen harajin da suke ƙaƙaba wa manoma a faɗin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Idi Barde Gubana ne ya bayyana hakan a zaman kwamitin zartaswa na jihar karo na 18 da aka gudanar a ranar Laraba.

Gubana wanda ya wakilci Gwamna Mai Mala Buni ya ce taron gaggawar na zuwa ne bayan sabbin hare-hare da ’yan ta’adda suka kai sansanonin soji, wanda ya ce ba ƙaramar barazana ce ga zaman lafiyar jihar ba.

Ya kuma bayyana damuwa kan hare-haren ‘yan ta’addan a garuruwan Yunusari, Geidam, da Tarmuwa, inda suke tilasta wa mutane da kuma manoma biyansu jangali da haraji.

“Idan za ku iya tunawa a baya-bayan nan an samu hare-hare da wasu sansanin sojojinmu da dama.

“Haka kuma ana tilasta wa mutanenmu biyan jangali da haraji musamman a ƙananan hukumomin Yunusari, Geidam, da Tarmuwa da sauransu.

“Mun taru a nan ne domin tattauna yadda za mu tabbatar mun kawo ƙarshen miyagun nan domin babban aikin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”

Gubana ya kuma ce duk da cewa jihar ta samu zaman lafiya na ɗan wani lokaci, hare-haren bayan nan na buƙatar jajircewar jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan sojoji da ‘yan sandan da aka kashe a harin makarantar horas da wasan kwaikwayo ta Arewa maso Gabas da ke garin Buni Yadi a Ƙaramar Hukumar Gujba.

Aminiya ta rawaito cewa harin na ranar Juma’a ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla sojoji da ‘yan sanda 36.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp