Rikicin Rasha da Ukraine: Kasar Burtaniya ta Daskarar da Kadarorin Mai Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea Roman Abramovich

Rikicin Rasha da Ukraine: Kasar Burtaniya ta Daskarar da Kadarorin Mai Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea Roman Abramovich

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kakaba takunkumi kan gwamnatin Putin da magoya bayansa, Burtaniya ta sake daukar mataki.

Ta sanya takunkumi kan mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tare da bayyana shi a matsayin dan tsagin Putin.

Wannan na zuwa ne lokacin da kasar Ukraine ke ci gaba da fuskantar hare-haren bama-bamai daga kasar Rasha.

Kasar Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich, kana ta sanya haramcin mu’amala da daidaikun mutane da ‘yan kasuwa na Burtaniya, da dokar hana zirga-zirga duk dai akansa.

Sky Sports ta rahoto Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson yana cewa:

“Ba zai yiwu a samar da mafaka ga wadanda suka goyi bayan mummunan harin da Putin ya kai wa Ukraine ba.”

Hakazalika, ya kara da cewa:

“Takunkumin na yau shine mataki na baya-bayan nan na goyon bayan da Birtaniya ke baiwa al’ummar Ukraine ba tare da kakkautawa ba.

“Ba za mu sassauta ba wajen kuntatawa wadanda suka taimaka wajen kashe fararen hula, lalata asibitoci da kuma mamaye wasu ‘yan uwa ba bisa ka’ida ba.

Har ila yau, sakatariyar harkokin wajen Burtaniya Liz Truss ta ce:

“Takunkumin na yau ya sake nuna cewa ‘yan kama karya da masu cika aljihu da kudin kasa ba su da wani matsayi a cikin tattalin arzikinmu ko kuma al’ummarmu. Kusancinsu da Putin ke nuna suna da hannu wajen ta’addancin nasa.

“Jinin al’ummar Ukraine na hannunsu, ya kamata su rataye kawunansu saboda kunya.

“Goyon bayanmu ga Ukraine ba zai kassara ba. Ba za mu tsaya wata-wata ba a wannan aiki na kara matsi kan gwamnatin Putin da kuma kassara kudaden na’urar yakinsa na zalunci ba.

Karin bayani na nan tafe…

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 34 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 15 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here