Rundunar Sojin Najeriya ta ce Dakarunta sun bankado Naira Miliyan 60 da ake kokarin kai wa ‘yan ta’adda kudin fansar karbo wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Haka kuma, dakarun sun yi nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su da suka hadar da mata da kananan yara.
Dakarun, wadanda suka hada da sojin sama da na kasa, sun kai ga cin karfin ‘yan bindigar. Inda suka bankado tare da kwato muggan makamai da bindiga kirar AK47, da albarusai da sauransu.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewar, cikin wadanda ake zargin zasu kai kudin fansar akwai jami’in tsaro na farin kaya wato DSS.
Read Also:
Wani jami’in liken asiri ya shaidawa PRNigeria cewa dakarun sojin saman bataliya ta 271 a Birnin Gwarri, da Dakarun FOB na Gwaska, sun kubutar da dimbin mutanen da aka yi garkuwa da su a yayin atisayen na hadin gwuiwa.
Jami’in ya ce: “An kwato zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 60, Man Fetur da kuma muggan makamai, a yayin gudanar da aikin.
“Sauran kayayyakin da sojojin suka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hadar da Motoci, Bindigu kirar AK-47 Alburusai iri-iri da kuma wayoyin hannun.
“Za kuma a mika batun jami’an tsaron da suka hada da na DSS da ake zargi da kai kudin fansar ga ma’aikatar tsaron Najeriya, domin gudanar da bincike.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 25 minutes 52 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 7 minutes 17 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com