Home Labarai Sojoji Sun Lalata Matatun Mai Guda 40 Dake Aiki Ba Bisa Ka’ida...

Sojoji Sun Lalata Matatun Mai Guda 40 Dake Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Yankin Niger Delta

Dakarun sojin Operation Delta Safe sun sami nasara tarwatsa matatun Mai guda 40 dake gudanar da aikin tace mai ba bisa ka’ida ba a jihar Delta dake kudancin Nijeriya.

Daraktan yada labaran rundunar sojin kasar Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi na mako-mako kan yunkurin dakarun sojin kasar na kawar da dukkan wasu ayyukan ta’addanci da muggan dabi’u.

Onyeuko ya kara da cewa kimanin litar danyen Mai 1,107,400 da kuma litar AGO 456,450 sojojin Nijeriyar suka sami nasarar kwatowa a yayi atisayen.

Yace “a cikin dan kankanin lokaci sojojin sun bankado tare da lalata matatun mai guda 40 dake aiki ba bisa ka’ida ba, da kuma tankunan ajiyar main a karfe guda 165 sai kuma wasu ramukan ajiyar mai guda 23 da jirgin ruwa na katako  guda 5 dake dauke da man.

“Dukkan  abubuwan da aka kwato da kuma masu aikata laifi da aka kama an mika su ga hukomomin dake suka dace domin cigaba da daukar mataki”

Haka zalika Oyeuko, ya bayyana cewa dakarun da ke aiki a karkashin rundunar OCTOPUS Grip na kara matsa lamba kan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da sauran masu aikata laifuka, wanda hakan ya kassara barayin mai a kasar.

“Operation OCTOPUS GRIP hadin Gwuiwa da dakarun DELTA SAFE sun gudanar da wasu atisaye a wasu rafukan, garuruwa da suka hadar da Jesse, hanyar Warri dake karamar hukuma Eithiope ta yamma, Banga, Mondongho Rafi a karamar hukumar Warri ta Kudu Maso Yammacin Jihar Delta da dai sauran yankuna.

Ya kara da cewa “Sauran wuraren sun hadar da rafin Okubotowa dake karamar hukumar Akassa Brass, Ikebiri ta kuduncin karamar hukumar Ijaw ta jihar Bayelsa akwai yankunan Gwathrone da ke karamar hukumar Bonny ta Jihar Rivers, da karamar hukuma Akpabiyo a Jihar Cross River da kuma Effiate Waterway Ibaka a jihar Akwa Ibom”.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp