Dakarun sojin saman Nijeriya sun sami nasarar halaka mayakan kungiyar Boko Haram tsagin ISWAP, a yakin Arewa Maso Gabashin kasar kamar yadda PRNigeria ta rawaito.
Mayakan da dakarun suka halaka da sanyin safiyar Litinin sun sanya shingen tsare ababa hawa a hanyar Goni Masari dake kusa da hanayar Maiduguri zuwa Damaturu, a jihar Borno.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Dakarun rundunar sojin sun sami wani rahoton sirri daya bayyana yadda mayakan suka tare kan hanyar wanda tuni har sun sami damar yin garkuwa da wani matukin mota, nan basuyi kasa a gwuiwa ba suka farmake su da jiragen yaki.
A cewar kwmandan daya jagoranci kai harin yace dakarun sojin sun sami nasarar kubutar da wanda akayi garkuwa dasu su 5, a harin da suka kai wa ‘yan ta’addan.
Kwamandan, wanda ya ki bayyana sunansa ga PRNigeria, yace sojojin sun halaka mayakan kungiyar ta ISWAP sama da 13, tare da raunata wasu da dama, inda suka sami nasarar kwato motar dake dauke da bindiga da suka bari a wajen.
By PRNigeria












