KORAFI: Wasu hotuna da suka dauki hankulan al’umma da aka yada a kafafen sada zumunta na Facebook da whatsapp sun nuna yadda Dan takarar Mataimakin shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC Senator Kashim Shettima, yake Karin kumallo da ‘yan bindiga.
CIKAKKEN BAYANI: wasu hotuna sun yadu a kafafen sada zumunta, wanda suke nuna yadda sanator Kashim Shatima, kma tsohon gwamnan jihar Borno, wadanda ke nuna yadda ya dauki hoto da wasu da ake zargin mayaka masu tada kayar baya ne, wanda aka nuna sun a cin tsire da biredi da kuma Ruwan roba.
Hoton da aka yi masa take “yan bindiga na Karin kumallo da Mai gidan su. Chanki waye? Mataimakin Tinubu, Kashim Shettima.”
An sami zazzafan ce-ce-kuce tsakanin mabiya addinin Kirsita da Musulmi tun bayan da aka sanar da Musulmi a matsayin wanda zai yiwa Dan takarar shugabancin kasar karkashin inuwa jam’iyyar APC mataimaki. Wasu daga cikin mabiya addinin kirsitanci a kasar sunyi ikirarin cewa ba adalci bane dan takarar shugaban kas ana Jam’iyyar APC ya zabi wanda zai tsaya takarar dashi daga cikin mabiya addinin Musulunci kasancewar addinin su daya duba da yadda kasar take
RA’AYIN MAI BINCIKE: tun bayan ayyana sanata Kashim Shettima matsayin mataimaki ga dan takarar shugaban kas ana jam’iyyar APC Asiwajo Ahmad Tinubu, wasu cikin Al’ummomi suka fara nuna cewa an yi son kai a zabin nasa, gami da kalubalantar hadin.
Guda cikin irin wadannan kalaman kalubalanta kuwa, an dingi yada wasu hotona na sanata shettima tare da wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne ko kuma ‘yan Ta’adda.
BINCIKEN TABBATARWA:
Read Also:
Ta cikin wani cikakken faifen Bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu Sanata kashim Shettima yana cin abinci tare da Fulani makiyay a yankisu, lokacin da ya kai musu wata ziyarar lallashi a kokarinsa na shawo kan su, su sanya ‘ya’yan su makaranat domin su ci gajiya tsarin nan na Ilimi kyauta a wannan yanki, wannan faifen bidiyon ke nuna Zahiri sanata Kashim ne.
A kuma wannan ziyara ne shatima ya sami damar cin abinci tare da wadancan shuwagabannin Fulani.
Faifen bidiyan kuwa yayi masa taken “Muna Shigar da yaran Fulani makiyaya Makaranta a karkashin shirn bayar da tallafin Karatu kyauta.
“ A karkashin wannan Shirin, muna jan hankalin iyaye da yara tare da Dimbin Al’ummar dake wannan yanki don yin rijiistar shiga wannan tsari.
Idan za’a iya tunawa, a watan Oktoban 2017 ne Gwamnan Jihar Borno na wancan lokaci, kashim Shettima ya kaddamar da Shirin baiwa ‘ya’yan Fulani Makiyaya rijistar a makarantu kyauta, tare da jan hankalin Fulanin don ganin an dakile yawan fadace-fadace dake haifar da rashin zaman lafiya a cikin Al’umma.
Haka kuma ko da a watan Disambar 2018, Uwar Gidan Shugaban kasa Muhammad Buhari Aishata kaddamar da bude makaranta wadda aka sanaya mata suna “Aisha Buhari Integrated School for Nomadic community” a garin Maduguri.
Makarantar wacce Gwamnatin Borno karkashin jagorancin Kashim Shettima ta samar da ingantattun kayan aiki, gani da inganatccen yanayi domin koyo da koyarwa.
Shettima ya gana da iyayen yaran da dama, haka kuma an dauki lokaci ana wayar da kai tare da karawa Fulani makiyaya kwarin gwuiwa, abinda ya sanya Fulanin bada yaransu da dama domin saka su a makarantar, hakan kuma ya taimaka matuka wajen kawar da tashe tashen hankula daya ke da alaka da faulani makiyaya a jihar ta Borno.
HUKUNCI/ DAGA KARSHE
Maganar cewa Sanata Kashim Shattima ya yi Karin kumallo da ‘yan fashin, KARYA ce. Dangane da hujjojin da PRNigeria ta tatta daga Faifan Bidiyon da tayi masa kallon kurulla tare da tattara rahotannin daga wasu kafafen yada labarai, sanata Kashin Shettima bai taba cin abincin safe ( Karin kumallo) da ‘yan ta’adda ba.Don haka Da’awar ba GASKIYA ba ce.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 41 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com