Home Labarai 2023: Kungiyar Can Ta Bukaci INEC Ta Gudanar Da Sahihin Zabe

2023: Kungiyar Can Ta Bukaci INEC Ta Gudanar Da Sahihin Zabe

Gabatowar kakar zaben 2023, kungiyar Kiristoci ta Nijeriya wato (CAN) dake fadin jihohi 19 na Arewa gami da birnin tarayya Abuja ta bukacin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, kan ta tabbatar da zaben 2023 ya kasance sahihin zabe mai cike da adalci.

Haka kuma kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari, da ya bayar tarihi mai kyau bayan ya sauka daga karagar Mulki ta hanyar tabbatar da kyakkyawan sauyi a shekarar 2023.

Wannan na kunshe ta cikin wata takardar bayan taron majalisar zartarwar kungiyar a jihar kaduna, taron bisa jagorancin shugaban kungiyar reverend Yakubu Pam da sakataren kungiyar  Elder Sunday Oibe, inda sanarwar tace wadanda ke kassara tattalin arzikin kasa zasu yi amfani da yunwa matsayin makami a babban zaben 2023 mai zuwa.

Kungiyar ta bukaci Gwamnati a kowanne mataki data dauki gabarar magance dukkan matsalolin talauci da yunwa dake addabar Al’umma Nijeriya.

“Muna kira ga Al’umma Nijeriya dasu tabbar an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tashin hankali ba. zabe ba yaki bane. Babu wani dan siyasa da zai yadda ya mutu, don haka kada kowa ya dauki doka a hannun sa.

“Dole ne ‘yan siyasa su gudanar da harkokin sun a siyasa bisa tanadin doka da oda, ba tare da nuna kyama ba, dole ne shuwagabanni jam’iyya, ‘yan Takara, ‘yan jam’iyya , magoya baya, su mayar da hankali yayin yakin neman zaben su da kalaman da zasu taimaka wajen magance kalubalen dake addabar kasa nan.

“Kungiyar CAN ta reshen Arewa na kira ga matasa, kada su yadda wani dan siyasa yayi amfani da su wajen tada husuma, idan kun lura ‘ya’yan sun a can suna karatu a ketare, ya kamata iyaye su ja kunnen ‘ya’yan su da kada ‘yan siyasa su dauke si aiki a matsayin ‘yan daba,” inji sanarwar.

Haka kuma kungiyar ta nuna damuwar ta kan yajin aikin kungiyar malaman jami’oin Nijeriya ta ASUU da ya dauki lokaci, inda tayi kira ga Malaman da Gwamnatin tarayya kan su samar da matsaya guda domin cigaban dalibai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp