Dakarun sojojin Nijeriya sun sami nasarar kame wani dan Boko haram tsagin ISWAP daya kware a fannin kerawa da gyaran bindiga a kauyen Gorom dake karamar hukumar Monguno a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata takardar sanarwa da shalkwatar rundunar ta aikewa PRNigeria mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran rundunar sojin Nijeriya Manjo Janar Musa Danmadami,
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar tace a ranar 26 ga watan satumba zuwa 3 ga watan Oktoban wannan shekara dakarun sojojin sun sami nasara kame shi, dauke da gidan shirya alburushi guda 300 babu alburushin a ciki, wanda ake zargin yin amfanin dasu wajen shirya alburushin mai tsayin 7.62mm.
An dai zargi kwararren makerin bindigar ne da kasancewa guda cikin masu bada bayanan sirri ga mayakan Boko Haram tsagin ISWAP a wurare daban-daban, haka kuma rundunar ta sami nasarar cito ‘yan matan Chibok 2 da suka hadar da Yana Pogu da rejoice Senki wanda ke da lamaba ta 19 da 70 cikin jerin jadawalin ‘yan matan Chibok da aka sace da ‘ya’yan s a kauyen Bula Davo dake karamar hukumar Bama da kauyen Kawur dake Karamar Hukumar kunduga a jihar Borno gami da wasu wadanda aka sace su 12.
PRNigeria Hausa












