Home DUNIYA Majalisar Dinkin Duniya Tayi Tir da Mamayar Rasha Kan Ukraine

Majalisar Dinkin Duniya Tayi Tir da Mamayar Rasha Kan Ukraine

Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar yin tir da Rasha kan mamaye wasu sassan Ukraine da ta yi, matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce sako ne mai karfi ga takwaransa Vladmir Putin.

Kasashe 143 ne suka goyi bayan kudurin na yin tir da Rasha a zauren Majalisar Dinkin Duniyar, inda 5 suka hau kujerar naki, sauran kasashe 35 kuma suka kauracewa zaman, wadanda suka hada da China, India, Afirka ta Kudu da kuma Pakistan, duk da matsin lambar da Amurka ta rika musu kan su yi tir da Rashan; kamar yadda jaridar Reuters ta ruwaito.

Kudurin dai ya yi tir da matakin Rasha, na shirya  zaben raba gardama a cikin iyakokin Ukraine” da kuma “yunkurin mamaye yankuna hudu na kasar ta karfin tsiya da shugaba Vladimir Putin ya sanar a watan jiya.

Ko a watan Satumban da ya gabata, sai da Majalisar ta nufaci kada makamanciyar kuri’ar amma Rasha ta yi amfani da kujerarta wajen dakile yunkurin duk da matakin Amurka na kafiya don tabbatar da ganin an yi tir da Moscow.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp