Kalaman ministan ilimin Nijeriya Adamu Adamu na cigaba da yamutsa hazo a kasar, inda wa suke ganin cewa kamata yayi ace ya ajje mukamin tun da fari daya fahimci gazawar tasa.
Tun da fari dai yayin wani taron majalisar iimi ta kasa karo na 66 ranar alhamis a birnin tarayya abuja an jiwo ministan na bayyana cewa ya gaza a matsayin sa na ministan ilimi a kasar.
Read Also:
Wannan kamalami na ministan na zuwa ne bayan gazawa da yayi wajen warware kalubalen da dama daya kamata ya warware kasancewar sa minister mafi dadea akan harkokin ilimi a kasar.
Sai dai yayin jawabin ya zargi ma’aikatun ilimi na jihohi da kara ingiza wasu abubuwa da suka taimaka wajen gazawar ta sa matsayin ministan ilimi.
Yace kama daga kan karin yawan yaran da basa zuwa makaranta da aka samu a kasar har zuwa ga kalubalen kungiyar malaman jami’oin kasar ta ASUU da sauran da sauran matsalolin dake kara tabarbara harkokin ilimi manyan makarantu, wanda ya gaza samar da mafitar shawo kan matsalolin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 11 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 53 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com