EFCC ta Cafke Mustapha Naira Mai Canjin Kudi a Abuja

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta cafke wani mutum mai suna Mustapha Muhammad, wanda aka fi sani da  Mustapha Naira bisa zargin yada jita-jita a fannin harkokin kudi a kasar.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da hukumar ta ranar talata, wanda hukumar ta bayyana cewa ta kama shi ne ranar 12 ga watan nuwamba a yankin wuse zone B wadda ke matsayin cibiyar hada-hadar kasuwancin chanjin kudi a birnin tarayya Abuja.

Hukumar tace kame na guda cikin ayyukan da ta ke yin a tsaftace harkokin chanjin kudaden waje da kuma kawar da dukka masu kawo tasgaro a fannin da kuma yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasar.

“wanda ake zargin yayi wasu bayanai masu amfani a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da bincike” a cewar EFCC.

Idan dai za’a iya tunawa hukumar EFCC ta kai sumame kasuwannin chanjin kudi, dake Nijeriya da suka hadar da jihohin legas, kano dama birnin tarayya kasar Abuja, wani bangare na dakatar da sauyin kudin kasar da Dalar Amurka abinda ake kallon ya kara sanya farashin dalar tashin gwauron zabi.

An zargi yadda wasu ke halasta kudin haram ta hanyar sauya su da dala, da nufin kada su yi asarar su sakamakon sake fasalin kudin kasar da Gwamnati tayi Shirin yi.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 21 hours 5 minutes 32 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 22 hours 46 minutes 57 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com