Wani jami’i a Malawi ya ce aƙalla mutum 40 ne suka mutu sakamakon mummunar ɓarnar da wata guguwa mai ƙarfi haɗe da ruwa da ake yi wa laƙabi da ‘Freddy’.
faya-fayen Bidiyoyin da aka ɗauka sun nuna yadda rufin gidaje da dama suka ɗaye a wani mummunan ɓarna da ruwan saman yataɓa yi a biranen ƙasar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kawo yanzu ba a kai ga tantance yawan ɓarnan da guguwar haɗe da ruwa mai ƙarfi suka yi a sassan yankunan ƙasar ba.
Ko a ranar Lahadi ma wata guguwar mai ƙarfi haɗe da ruwan sama ta shafi wasu yankunan ƙasar Mozambique, karo na biyu a cikin ƙasa da wata guda.
Hukumomin ƙasar sun ce aƙalla mutum shida ne suka mutu a birnin Quelimane.
Binciken farko da aka gudanar kan ɓarnar da guguwar ta yi, ya nuna cewa gidaje da dama sun rushe a fiye da rabin lardunan ƙasar.
PRNigeria Hausa











