Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma fadar gwamnatinsa da ke Abuja, bayan shafe kwanaki a mahaifarsa Daura ta jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan na cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta Twitter, inda ya ce shugaban ya koma Abuja ne bayan kwanaki 18.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Saƙon ya ƙara da cewa shugaban ya yi amfani da lokacin wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa tare da ziyara da ya kai Maiduguri da taron Majalisar Dinkin Duniya da ya halarta a birnin Doha na ƙasar Qatar.
Garba Shehu ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan ne cikin wannan makon shugaban tare da sauran ma’aikatan fadarsa da suka yi rajistar zaɓe a Daura za su sake komawa domin halartar zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi.
PRNigeria Hausa












