Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Najeriya NBC ta sanyawa wasu kafafen yada labarai 25 takunkumi sakamakon karya dokokin hukumar a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Daraktan hukumar na kasa Balarabe Shehu Illele ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya kara da cewa hukumar ta kuma baiwa wasu kafafen yada labarai 16 gargadi domin su gyara ayyukansu.
Ya kara da cewa wasu daga cikin wadannan kafafen yada labaran sun baiwa baki da masu fashin baki har ma da masu kiran waya a yayin shirye-shirye damar furta wasu kalmomi mara sa da dadi ba tare da yi musu linzami ba.
Balarabe Illela ya kuma bukaci sauran kafafen yada labaran kasar da su mayar da hankali wajen sanya kwarewa da kuma bin doka da oda yayin gudanar da ayyukansu.
PRNigeria Hausa












