Mayakan M23 sun fara janyewa daga yankunan da suka kwace a Congo

Rahotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo na cewa mayakan ‘yan tawayen M23 sun fara janyewa daga yankunan da suka kwace iko da su a gabashin kasar, matakin da ke zuwa bayan jibge karin dakarun kasashen ketare a yankin.

Majiyoyin Soji da na fararen hula sun tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP batun janyewar mayakan na M23 wadanda a baya suka kwace garuruwa da dama a lardin na arewacin Kivu da ke gabashin kasar bayan gwabza yaki na tsawon watanni tsakaninsu da dakarun gwamnatin Congo.

Shugaban mayakan sa kai na garin Mweso da ke yankin Masisi mai tazarar kilomita 100 da birnin Goma fadar gwamnatin lardin na Kivu, Alphonse Habinna ya shaidawa AFP ta wayar tarho cewa basu da masaniya kan dalilin janyewar dakarun.

Sai dai duk da wannan janyewa, Mayakan na M23 na kuma ci gaba da gwabza fada tsakaninsu da dakarun Congo wadanda ke samun taimakon sojojin kasashen gabashin Afrika 7 a yankuna da dama bayan lardin na Kivu.

Duk da shiga tsakanin da Rwanda ta yi wanda ya kai ga kulla yarjejeniyar tsagaita wuta, bangarorin biyu sun koma kai wa juna farmaki kasa da mako guda bayan cimmajituwar a ranar 7 ga watan nan, inda a baya-bayan nan M23 ta yi barazanar katse hanyar da ta hada iyakokin Congo da Rwanda bayan karakarfin da sukayi a gab da birnin Goma.

Wannan mataki na M23 na zuwa ne a daidai lokacin da jami’na diflomasiyya ke tsaka da tattaunawa a kokarin kawo karshen yankin na tsawon shekara guda da ya tagayyara tarin iyalai.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 29 minutes 3 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 10 minutes 28 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com