Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya kaɗa ƙuri’ar a akwatinsa mai lamba 041 a mazabar Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.
Dakta Nasiru Yusuf Gawuna shi ne mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma yake yi wa jam’iyyar APC mai mulkin jihar takarar kujerar gwamna.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Har wayau kuma a wata rumfar zaɓe mai lamba 47 da ke Hausawa a karamar hukumar tarauni a jihar Kano an sami tsaikon harya zuwa ƙarfe 9 na safe mai kaɗa ƙuri’a ɗaya ce kawai ta bayyana a rumfar.
Ita ma ta ce sai da ta yi tafiyar tsawon kilomita huɗu kafin isa rumfar zaɓen kasancewar babu abin hawa.
PRNigeria Hausa












