Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya NBC tace tarar kafar yada labari ta Channels TV bisa wata tattaunawa da tayi da wanda ya yi wa Jam’iyyar LP takarar mataimakin shugaban kasa a kakar zaben shekarar 2023 Baba-Ahmed.
Ta cikin Shirin Politics Today na makon daya gabata Baba-Ahmed ya bukaci babban Alkalin alkalan Nijeriya Olukayode Ariwoola da kada ya rantsar da Bola tinubu matsayin shugaban kasa.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar na Jam’iyyar LP yace babu zababben shugaban kasa saboda Tinubu bai cika ka’idojin tsarin Mulki ba.
Read Also:
Kamfanin dillancin labaru na Nijeriya NAN ya rawaito cewa tarar na cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 27 mai dauke da adreshin baban daraktan tashar na Channels.
shugaban hukumar ta NBC yace za ta iya tunzura jama’a tare da kawo hargitsi a ƙasar, don haka a cewar hukumar, ta saɓa wa dokokin yaɗa labarai.
lllelah ya ci gaba da cewa a lokuta da dama, hukumarsa ta sha faɗa wa gidan talabijin ɗin ya riƙa la’akari da zaman lafiyar ƙasar, kafin yaɗa kowanne irin shiri nasa.
Don haka ya ce hukumar ta sanya wa gidan talbijin ɗin tarar naira miliyan biyar a kan wannan saɓa ƙa’ida, tare da gargaɗin Channels TV ya kiyaye aukuwar irin hakan a nan gaba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 36 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 17 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com