Dakarun sojojin Nijeriya runduna ta daya dake aiki a karamar hukumar Chikum a jihar kaduna, sun sami nasarar fatattakar ‘yan bindiga biyar tare da kwato bindigu kirar Ak-7 guda 6 da kuma gidan Alburusai na bindigar AK47 guda shida da kuma wani Alburushi masu tsayin 7.62mm guda 24.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin mai Magana da yawun rundunar shiyya ta daya Lt-Col Musa Yahaya ya fitar a jihar Kaduna.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Yahaya ya bayyana cewa dakarun sun gudanar da atisayen a yankin kan tudun Kaso da kanti zuwa Tantatu a dajin Kubusu dake jihar.
Yace atisayen ya kasance wani bangare na dakile ayyukan ‘yan fashi da masu aikata laifuka domin inganat tsaro da dawo da tattalin arziki mai dorewa a ‘yankin.”
Yahaya ya kara da cewa an fara atisayen ne a tsakar dare juma’a wanda ya sanya ‘yan bindigar suka jigata matuka.
Inda y ace sun sami nasarar kwato Babura hawa guda 3, wayar salula guda biyu da sauran kayayyakin amfani.
PRNigeria Hausa












