Rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya sun lalata sansanin ‘yan kungiyar awaren IPOB da takwararta ta ESN a Asaba da ke jihar Delta.
Wannan na Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta ce jami’anta sun kaddamar da samame kan sansanin ‘yan awaren da ke tsakiyar babban dajin Asaba da safiyar ranar Asabar, inda suka samu nasarar kwato makamai.
Sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar a lokacin samamen, inda daga bi-sani ‘yan bindigar suna gudu daga maɓoyar tasu.
Read Also:
Sanarwar ta ce sojojin sun kama daya daga cikin mayaƙan ‘yan awaren, tare da ƙwato bindigogi biyar kirar AK-47, da manyan bindigogi masu sarrafa kansu uku. da wata ƙirar G3 da ƙamar bindiga guda.
Sauran abubuwan da dakarun sojin suka ƙwato, sun hadar da kwanson saka alburushi biyar, da gatari da kuma tutar kungiyar IPOB.
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yaba da namijin ƙoƙarin da sojojin suka yi tare da sauran jami’an tsaro, a yunƙurinsu na kawar da ayyukan ‘yan bindigar da ke addabar yankin, tare da maido da zaman lafiya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 7 minutes 19 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 48 minutes 44 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com