Almundahana – Abba Gida Gida zai binciki Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamatocin bincike biyu domin duba batun wadaƙa da kuɗin al’umma da rikicin siyasa da ɓatan mutane tsakanin 2015 da 2023 a tsukin zamanin mulkin mutumin da ya gada, Abdullahi Ganduje.

Yayin ƙaddamar da kwamatocin ranar Alhamis, gwamna Yusuf ya buƙaci mambobin da su yi aiki domin hukunta wanda yake da hannu.

Gwamnan ya ce gudanar da bincike kan almubazzaranci da kuɗaɗen al’umma wani ɓangare ne na alƙawarin da ya ɗauka a lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki na bankaɗowa tare da gurfanar da mutanen da ke da hannu a rikice-rikicen siyasa da suka faru a jihar.

Ya bayyana yadda tashin hankali sakamakon rikicin siyasa ke janyo koma-baya ga dimokraɗiyya a faɗin duniya da kuma janyo asarar rayuka da rashin yarda a ɓangaren mutane da kuma waɗanda ke jagoranci.

Gwamnan ya ce bai kamata a ƙyale munanan rikice-rikicen siyasar da aka gani musamman a 2023 su wuce ba don a hana afkuwar haka a gaba.

Kwamitin farko, ƙarƙashin Zuwaira Yusuf zai duba rikicin siyasa da mutanen da suka ɓata daga 2015 zuwa 2023.

“Muna fatan a zaƙulo mutanen da ke da hannu tare da bayyana waɗanda suka tallafa domin su fuskanci hukunci a kuma gano dalilai da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da 2013”. in ji gwamnan.

Kwamiti na biyu, bisa jagorancin Mai shari’a Faruk Lawan, ya samu umarnin gwamna Yusuf da ya duba ƙararrakin da suka shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.

Gwamnan ya buƙaci mai shari’a Lawan da mambobin kwamitin da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen gano almubazzarancin da aka yi musamman a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata.

A zaɓen da ya gabata ne aka kama, ɗan majalisar wakilai Alhassan Doguwa saboda zargin hannu a kisan da aka yi wa wasu da kuma tayar da rikici, Sai dai daga bisani an ba da belinsa.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 39 minutes 5 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 20 minutes 30 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com