Dalilin haramta amfani da Maganin Benylin a Nijeriya – NAFDAC

Hukumar kula da inganci abinci da magunguna a Najeriya, NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara da ake kira Benylin wanda kamfanin Johnson & Johnson saboda yadda gwajin da aka yi ya gano illar da ke tattare da maganin.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukumar, NAFDAC ta ce gwajin da aka yi kan maganin ya nuna cewa yana ɗauke da sinadrin Diethylene glycol da aka gano yana haddasa cututtuka a bakin dabbobin da ake gwaji a kan su.

Ana amfani da Benylin Paediatric ne domin maganin tari da cushewar ƙirji da kuma maganin zazzaɓi da sauran matsaloli a yara ƴan shekara biyu zuwa 12.

Sinadarin Diethylene glycol na da illa ga bil adama idan aka sha kuma yana iya janyo asarar rai. Illar shan sinadarin ya haɗa da ciwon ciki da amai da gudawa da rashin fitar da fitsari da ciwon kai da matsalar ƙwaƙwalwa da ciwon ƙoda da ka iya kai wa ga rasa rai.

Bayanan da ke jikin maganin sun nuna maganin na kamfanin Johnson & Johnson ne, wanda yake Cape Town a Afirka ta Kudu.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 37 minutes 47 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 19 minutes 12 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com