Shugaban EFCC- Zan yi murabus Muddin na gaza gurfanar da Yahaya Bello a gaban Kotu

Shugaban hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa, Ola Olukoyede ya sha alwashin yin murabus idan ya gaza gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

ya bayyana hakana ne a wani taron tattaunawa da zaɓaɓɓun editoci a hedikwatar hukumar da ke Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban hukumar ya yi alƙawarin hukunta duk masu kawo tarnaƙi ga kama tsohon gwamnan.

A ranar 18 ga watan Afrilu, EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zarginsa da badaƙalar kuɗi masu tarin yawa.

Yahaya Bello dai bai bayyana gaban kotu ba tun bayan ayyana ana nemansa ruwa a jallo.

Shugaban EFCC ya ce da kansa ya kira Bello cikin mutunci inda ya nemi da ya bayyana gaban hukumar ya kuma yi bayani kan tuhume-tuhumen da ake masa. haka kuma Shugaban na EFCC ya ce duk da kiran wayar, tsohon gwamnan bai amsa gayyatar ba.

Yahaya Bello dai ya musanta gayyatar da aka yi masa inda ya ƙalubalanci EFCC ta gabatar da kwafin takardar gayyatar da ta aike masa.

Cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran tsohon gwamnan ya fitar, Yahaya Bello ya zargi EFCC da yaɗa jita-jita.

Shugaban EFCC ya ce “Idan har ban ga ƙarshen binciken da ake yi wa Yahaya Bello ba, zan ajiye aikina a matsayin shugaban EFCC.

“Na gurfanar da tsoffin gwamnoni biyu da a yanzu aka ba su beli – Willie Obiano da Abdulfatah Ahmed. Da mun bi Bello tun Janairu amma muka jira umarnin kotu.

“Idan har na iya gurfanar da Obiano da Abdulfatah Ahmed da Chief Olu Agunloye, me zai sa ba zan gurafanar da Yahaya Bello ba?

Olukoyode ya kuma ce tsohon gwamnan ya kwashi dala dubu 720 daga asusun gwamnati kafin barin mulki domin biyan biyan kuɗin makarantar ɗansa.

Tsohon gwamna Bello ya roƙi babbar kotun tarayya a Abuja da ta soke izinin kama shi da aka bai wa EFCC ranar 17 ga watan Afrilu.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 14 hours 42 minutes 28 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 16 hours 23 minutes 53 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com