An kai hari tare da lalata wasu muhimman layukan jiragen ƙasa a Faransa

Kamfanin dake kula da  sufurin jiragen ƙasa na Faransa  SNCF, ya ce wasu da ba a san ko su waye ba, sun kai hari tare da lalata sassan titunan jirage masu tsala gudu, yayin da ya rage sa’o’i kaɗan a buɗe gasar wasannin Olympics da birnin Paris ke karɓar baƙunci.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP, kamfanin na SNCF ya bayyana farmakin a matsayin babbar barazana, la’akari da tasirin da ya riga yayi, domin tilas aka soke jigilar jiragen ƙasa zuwa sassan Faransa da dama, wanda kuma sai an shafe hutun ƙarshen mako kafin kammala gyara layukan dogon da aka lalata.

Kamfanin kula da sufurin jiragen ƙasan na Faransar ya shawarci fasinjoji da su ɗage lokutan da suka tsara na yin balaguro, su kuma ƙauracewa zuwa tashohin jiragen ƙasa har zuwa lokacin da za a tabbatar da tsaro.

Harin dai yafi shafar titunan jiragen ƙasan masu tsala gudu da ke jigila zuwa yankunan Arewaci da Gabashin ƙasar, yayin da jami’an tsaro suka daƙile yunƙurin da aka yi na lalata titunan da ke sadarwa zuwa yankin Kudu maso Gabashi.

Kimanin ‘yan wasa 7,500 ake sa ran sun hallara a birnin Paris domin nuna bajintarsu a gasar Olympics, yayin da ake kiyasta yawan ‘yan kallo zai kai dubu 300.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 48 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 29 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com