Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta sanar da kama wani Ahmed Tela, wanda take zargi da dinka tutocin kasar Rasha da wasu masu zanga-zanga ke amfani da su a lokacin zanga-zanga a Kano da wasu jihohin Arewa.
An kuma kama masu zanga-zanga kimanin 30 da ke dauke da tutocin tare da tsare su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar hukumar ta farin kaya (DSS) a wani taron manema labarai da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya shirya.
An hangi yadda wasu masu zanga-zangar ke fitowa kan manyan titunan Nijeriya musamman jihohin Kano, Kaduna, Bauchi da wasu jihohin Arewacin Nijeriya dauke da tutocin kasar Rasha musamman a wannan rana ta 5 da fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar.
Read Also:
An ga masu zanga-zangar dauke da tutocin kasar Rasha suna zagaya tituna suna rera wakoki daban-daban tare da wasu dauke da alluna.
Adejobi ya ce daga tutocin wasu kasashe a Najeriya, wadda aka kasa ce mai cin gashin kanta, laifi ne, inda ya kara da cewa wadanda aka kama da wadanda suka dauki nauyinsu za a tuhume su kamar yadda dokar kasar ta tanada kan laifukan da suka aikata.
“Da safiyar yau ne muka kama wani ‘Ahmed Tela’ daga karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, bisa laifin samar da tutocin kasar Rasha masu yawan gaske da ake baiwa matasan Najeriya domin su dagawa.
“Mun kama shi, Kuma muna kara farautar wasu musamman wadanda suka sa ka su. Kamar yadda nake magana da ku, haka abin ya faru a Kaduna. mun sami damar kama 30 daga cikinsu dauke da tutocin Rasha ” in ji babban jami’in ‘yan sandan.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 2 hours 26 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 4 hours 7 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com