Kungiyar dake yaki da cin hanci da daidaito na harkokin gwamnati SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki bashin dala biliyan 1.5 na bankin duniya da jihohi 36 suka karbo tare da babban birnin tarayya.
Kungiyar ta kuma bukaci Tinubu da ya binciki zargin karkatar da lamunin China na $3.121bn da gwamnatin tarayya ta tarba.
Read Also:
SERAP ta roki Shugaban kasa da ya umarci Babban antoni janar na kasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da hukumomin da suka dace da yaki da cin hanci da rashawa da su gaggauta yin bincike sosai kan yadda aka kashe rancen, ta yadda za a rage “talauci da inganta rayuwar al’umma a fadin jihohin kasarnan.”
Hakan na kunshe ne a wata budaddiyar wasika mai kwanan watan Agusta 10, 2024, mai dauke da sa hannun Mataimakin Daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 3 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 44 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com