Majalisar Dattijai ta yi wa Obasanjo Martani

Majalisar dokokin Nijeriya ta mayar wa tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo martani game da kalamansa kan kudaden albashin ƴan majalisar.

A ranar Juma’a ne dai tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo wanda ya sha sukar gwamnati ya yi zargi ƴan majalisar cewa su ke yanka kansu albashi mai tsoka da kuma hanyoyin da suke samu kuɗi fiye da ƙima.

A cewar tsohon shugaban, hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya ce ya kamata ta yanke hukunci kan albashin da kowane ma’aikaci zai karɓa.

A martaninta, majalisar dokokin ta ce duk abun da ake ba wa ƴan majalisar na kan tsari tare da cewa ba su ke yankawa kansu albashi ba.

sai dai ta cikin wata sanarwa da kakakin majalisar dattawa Yemi Adaramodu ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana ikirarin tsohon shugaban a matsayin “marar tushe”.

Wannan cacar baki na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya.

A shekarun baya baya nan ɓangaren majalisar dokokin Najeriya na daga ɓangaren gwamnati da galibin mutane musaman ma masu sharhi kan al’amurran yau da kullum da ƙungiyoyin fararen hula ke zargin cewa abubuwan da suke samu na wuce ka’idar da ya kamata a ce ana ba su a matsayin haƙƙoƙinsu na yi wa alumma dokoki.

Wasu ƙungiyoyi da ƴan Najeriya sun ta nuna tsaya ga ƴan majalisar a kan zargin yadda suke laftawa kansu kudin mazaɓu a kasafin kuɗi wanda wasu ke ganin sun fifita kansu.

A wasu lokutan ma wasu ƴan majalisar da kansu sun fito sun koka kan cewa ana nuna bambanci a rabon kuɗin mazabun.

A yanzu kuma tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ne ya soki ‘yan majalisar kan cewar suna yankawa kansu albashi da kuma samun kuɗi masu gwaɓi daga fadar shugaban kasa.

‘’Kudin jarida, alawus din ɗan kamfai da kudin bahaya, kuma kuna ba kanku abubuwa barkatai, cikin girmamawa kun san hakan ba daidai ba ne a ce ina yankawa kaina albashi, majalisar dattawa na yin haka, har ma tinkaho kuke yi da haka’’ in ji Obasanjo.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa ana bai wa dukannin ‘yan majalisar naira miliyan 200.

Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sa ido kan harkokin Majalisun dokokin kasar ya ce akwai ƙamshin gaskiya a kalaman tsohon shugaban kasar:

‘’Akwai wasu kudade da a duk lokacin da za su tafi aikace-aikace ba ya cikin alawus -alawus dinsu, baya cikin albashinsu , hatta taron jin bahasin jama’a suna karbar alawus- alawus’’ in ji shi

Rafsanjaji ya yi gargadin idan har ba a kawo karshen wannan matsalar ba, to ba za a daina rigimar siyasa da rigimar zabe ba.

A cewarsa “idan mutane sun san cewa idan suka zo majalisa za su sami irin wadannan makuɗan kudade na Halak da na haram to za a ci gaba da samun rikici lokacin zabe”

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 16 hours 19 minutes 57 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 18 hours 1 minute 22 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com