Akalla mutane 16 ne suka ake zargin sun mutu bayan wani kwale-kwale makre da mutane ya kife a jihar sokoto dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Dundaye inda hukumar agajin gaggauwa ta NEMA ta bayyana cewa akwai mutane 19 da suka tsira da rayukansu.
Kwale-kwalen na ɗauke da manoma ne inda zai kai su gonakinsu na shinkafa a ranar Lahadi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
An gano gawa guda, sannan kuma akwai mata da yara daga cikin waɗanda suka ɓace.
Masu ninƙaya da kuma masu kamun kifi na cikin waɗanda suka shiga aikin ceton.
Jami’ai sun ce jirgin ya ɗauko ninkin mutanen da ya kamata ya ɗauka ne.
A makon daya wuce ma wasu manoma 15 sun nitse bayan jirgin ruwan da ya ɗauko su ya kife a jihar Jigawa da ke arewacin Nijeriya.
PRNigeria Hausa












