Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta sanar a ranar Alhamis cewa, farashin kaya a ƙasar ya sauka a karon farko da kashi 33.4 cikin 100 a watan Yuli inda aka kwatanta da kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin shekarar da muke ciki.
Kayayyakin da farashin nasu ya sauka sun haɗa da shinkafa da masara da ƙwai da burodi da man fetur.
To sai dai kuma farashin makamashi na ci gaba da hauhawa a cikin shekara ɗaya da ta wuce a cewar hukumar.
Najeriya dai ta fara aiwatar da manufofin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar tun a bara.
Ƙasar ta dauki matakai kamar cire tallafin man fetur da kuma farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, naira.
Shugaba ƙasar Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen na da matukar muhimmanci kuma ya zama dole da nufin farfaɗo da tattalin arziƙin.
A farkon watan Augusta ne ƴan kasar suka gudanar da zanga-zanga a kan matsin rayuwa ta kwana 10 don matsawa gwamnati ɗaukar matakan sassauta al’amura.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 56 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 37 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com