Gwamnatin tarayya Nijeriya na shirin yin hadin gwiwa da Gwamnatin Kano, don samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta a jihar dake arewacin kasar.
Ministan makamashi na kasa Chief Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyara da ya kai jihar a yammacin ranar Alhamis, inda yace wannan kudiri zai taimaka matuka wajen kaucewa matsalolin wutar lantarki a jihar dake matsayin cibiyar kasuwanci a yankin da kuma kaucewa sake lalacewar wutar da ya jefa da dama cikin halin kakanakayi.
Wannan na zuwa ne bayan da aka kwashe tsahon kwanaki a yankin babu wutar ta lantarki, lamarin da ya shafi jihohi 17, abin da ya jefa al’ummar cikin duhu da asara mai yawa a fannin kasuwancin.
Hukumomi sun yi zargin cewa ‘yanbindiga ne suka tunkuɗe layin wutar da ke kai wa arewa maso yamma, da arewa maso gabas, da wani ɓangare na arewa ta tsakiya wutar.
Read Also:
Da yake jawabi a lokacin da ya tarbi ministan Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar Gwamantin Kano, Mal. Shehu wada Sagagi, ya nuna damuwar sa matuka kan halin da A’ummar jihar Kano suka shiga bisa daukewar wutar lantakin.
“daukewar wutar lantarkin nan ya saka al’ummar mu cikin mawuyacin hali wanda ya haifar da asarar mai dumbin yawa”
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar biyan diyya ga wadanda wannan lamarin ya shafa.
Da yake jawabi a yayin ziyarar ministan Manajan daraktan kamfanin rarraba wutar ta nan jahar Kano KEDCO Abubakar Yusuf, ya tabbatarwa da al’ummar Kano cewa kamfanin KEDCO ya shirya tsaf dan ganin an Samu wuta wadacciya a fadin jahohin Kano da Katsina da Jigawa.
Ministan ya ziyarci gidan rarraba wuta na Kumbotso da tashar wuta mai amfani da hasken rana ta zawaciki wato Bagaja Renewable Energy Company.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 44 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 26 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com