Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya ce Najeriya ta kama hanyar farfaɗowa daga matsalolin matsin tattalin arzikin da take ciki.
Shettima ya ce tattalin arzikin ƙasar na cikin gida wato GDP ya haɓaka da kashi 2.98 a rubu’in farko na wannan shekarar.
Read Also:
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin buɗe kasuwar duniya ta Legas ta bana, inda ya ƙara da cewa tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da su, an yi su ne domin haɓaka tattalin arzikin ƙasar.
Shettima, wanda mai taimaka masa na musamman kan ci gaban yankuna, Dr Marian Tomitope Marshall ta wakilta, ya buƙaci waɗanda za su halarci kasuwar duniyar su yi amfani da damar domin kawo hanyoyin inganta tattalin arziki.
Ya ce gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin samar da hanyoyin sauƙaƙa harkokin kasuwa, domin jin daɗin ƴankasuwa na ciki da wajen ƙasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 29 minutes 31 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 10 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com