Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda bisa samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminun Bello.
Alƙalan kotun guda huɗu a cikin biyar ne suka tabbatar hukuncin, inda ake yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan watsi da ɗaukaka ƙararta, kamar yadda mai shari’a Moore Adumein ne ya sanar da hukuncin a madadin sauran alƙalan.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kotun ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi rangwame ga Maryam alhalin ana ci gaba da sauraron shari’arta a gaban kotun ɗaukaka ƙara, kamar yadda tashar Channles ta ruwaito.
A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne kotu a Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin da kashe mijinta Bilyaminu Bello a gidansu na Abuja shekarar 2017.












