An ji harbe-harbe da fashe-fashe a kusa babban filin jirgin Nijar

A daren jiya ne aka ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Diori Hamari da ke babban birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Kafar LSI Africa ce ta ruwaito labarin daga wasu shaidun gani da ido, inda suka ce an fara jin ƙarar ne da misalin ƙarfe 12 na dare, sannan ya ɗan ɗauki lokaci ana yi.

Wasu faye-fayen bidiyo da suka karaɗe kafofin sada zumunta a ƙasar sun nuna yadda haske ya yi sama daga daidai yankin da ake jin harbe-harben.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton dai hukumomi a ƙasar ba su ce komai ba kan aukuwar lamarin, musamman kan musabbin harbe-harbe da fashe-fashen ko asarar da aka yi, da kuma ko an rasa rai.

Sai dai akwai rahotannin da ba a tabbatar ba da ke zargin wataƙila mayaƙa masu iƙirarin jihadi ne suka yi yunƙurin kai hari a filin jirgin.

Sai dai wasu na zargin ganin yanayin ƙarar wataƙila akwai yiwuwar wata matsala ce ta cikin gida da ba za ta rasa nasaba da boren sojoji ba, kamar yadda rahoton ya ƙara.

Nijar dai na fama da matsalolin rashin tsaro a cikin ƴan shekarun nan duk da cewa tana ƙarƙashin mulkin Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya karɓi mulki bayan juyin mulkin watan Yulin 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com