Home Labarai Shugaba Tinubu ya nada Jakadan da zai wakilci Nijeriya a Amurka

Shugaba Tinubu ya nada Jakadan da zai wakilci Nijeriya a Amurka

Bola Ahned Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin jakadu hudu, daga cikin 68 da Majalisar Dattawa ta amince da su a watan Disamban 2025.Tinubu ya tabbatar da nadin Ayodele Oke a matsayin jakadan da aka nada a Faransa, da kuma Lateef Are a matsayin jakadan da aka nada a Amurka.

Shugaban Najeriya ya kuma tabbatar da nadin Amin Dalhatu, tsohon jakadan Korea ta Kudu, a matsayin babban kwamishina da aka nada a Birtaniya.

Usman Isa Dakingari Suleiman, tsohon gwamnan Kebbi, shi ne jakadan da aka nada a Turkiyya,ƙasar da Shugaba Tinubu zai fara ziyara a mako na sama.

A cikin wata sanarwa da ya aike wa Ma’aikatar Harkokin Waje, Shugaba Tinubu ya bukaci ma’aikatar ta sanar da gwamnatocin kasashen hudu game da nadin jakadun, bisa ga tsarin diflomasiyya.

Mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan dabaru da hulda da manema labarai Bayo Onanuga,ya jaddada manufar shugaba Tinubu na ganin Najeriya ta shiga sahun manyan ƙasashe a fanin diflomasiyya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp