Home Labarai Babu gudu ba ja da baya kan zanga-zanga a Abuja – NLC

Babu gudu ba ja da baya kan zanga-zanga a Abuja – NLC

Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC a Najeriya, sun ce suna nan daram kan ƙudirinsu na gudanar da zanga-zangar da suka shirya yi a gobe Talata.

Sun ce za su yi zanga-zangar ne domin nuna goyon bayansu ga ma’aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Ƙasar Abuja, waɗanda ke neman a biya musu buƙatunsu.

Ƙungiyoyin na NLC da TUC sun umarci dukkan rassansu da majalisun jihohi a yankin na Abuja da ƙewaye, da su tabbatar sun halarci zanga-zangar lumana da doka ta amince da ita, wadda aka tsara za ta yi ranar Talata.

Wannan na zuwa ne duk da cewa rundunar ƴansandan Abuja ta shawarci ƙungiyoyin ƙwadagon da su dakatar da zanga-zangar, bisa dalilan tsaro.

Sai dai, sakataren tsare-tsare na ƙungiyar ta NLC, Nasir Kabir, ya shaida wa BBC cewa ba su da niyyar sauya matsaya kan ƙudirinsu na gudanar da zanga-zangar.

“Zanga-zanga ce ta lumana da nuna fushi da ma’aikata za su yi kan zalunci na wannan mutumi wanda yake ganin ya fi ƙarfin kowa. Mu dai bai fi ƙarfin mu ba, muna bayan ma’aikata.

“Idan ba a biya ma’aikata hakkokinsu ba da alawus-alawus da kuma inganta aikinsu ba, yajin aiki yanzu muka fara babu wanda zai janye,” in ji Nasir Kabir.

Rahotanni na nuna cewa ma’aikatan hukumar gudanarwar babban birnin Abuja, sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani tun a ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata, bisa zargin rashin biyan albashi, da rashin ƙarin girma da kuma lalacewar yanayin aiki.

Lamarin ya sa hukumar FCDA ta garzaya kotun masana’antu ta ƙasar, inda ta bayyana yajin aikin a matsayin wanda bai halatta ba tare da neman kotun ta hana ma’aikatan yajin aikin, sai dai kungiyoyin NLC da TUC sun sha alwashin tsayawa kai da fata wajen ƙwatowa ma’aikatan hakkokin su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp