Aƙalla masu haƙar ma’adinai 33 ne suka mutu sakamakon shakar iskar gas ta sinadarin carbon wace take guba mai ƙarfi yayin da suke hakar ma’adinai a Jihar Plateau, kamar yadda bbc ta rawaito.
Ana hasashen wannan mummunan lamari ya faru ne kafin fitowar rana a wani wuri a wajen garin Wase, wanda kamfanin ma’adinai na Solid Unity Nigeria Ltd, ke gudanarwa.
Ana ganin cewa guba mai ƙarfi ta sinadarin ta taru a cikin ramin ƙasa da iska ba ta samun shiga sosai, wanda ya sa ma’aikatan suka fadi a kasa kafin su kammala aikin dare.
Wadanda suka je aiki da safe ne suka tarar da gawawwakin.
Jami’an tsaro sun rufe wurin hakar ma’adinan, wanda ke kimanin kilomita 200 daga gabas zuwa kudu maso gabas na Jos, babban birnin Jihar Plateau, yayin da ake gudanar da bincike domin gano musabbabin zubar sinadarin.
Hukumomin jihar har yanzu ba su kai ziyara wurin ba, kuma rahotanni sun nuna cewa an samu cikkas wajen kai taimakon gaggawa saboda rashin tsaro a yankin.











