Home Labarai DSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a...

DSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a Edo

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kama mutum na shida da ake zargi da hannu a kitsa harin da aka kai a cocin Katolik na St. Francis da ke Owo a jihar Edo a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da masu ibada 40 tare da jikkata wasu da dama kamar yadda gidan talabijin na gwamnati NTA ya ruwaito.

Tun da farko, hukumar ta riga ta kama mutum 5 da, inda suke fuskantar shari’ar aikata laifukan ta’addanci, yayin da mutum na shida da aka kama na baya-bayan nan, mai suna Sani Yusuf, ya shafe kusan shekara huɗu yana ɓuya kafin a kama shi a wata unguwa mai suna Iguosa da ke ƙaramar hukumar Ovia North Local Government Area a jihar Edo.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa Yusuf wani babban kwamanda ne a ƙungiyar ISWAP kuma bayan harin Owo ya tsere zuwa Kano kafin daga bisani ya koma ɓuya a yankin na Edo.

Rahotanni sun ce ya amsa laifin yana da hannu a harin da aka kai cocin da kuma wasu hare-haren ƙungiyar, ciki har da farmakin da aka kai a barikin sojoji na Suleja a watan Yulin 2022 da kuma sace-sacen mutane a Kaduna da kewaye.

“Ya kuma amince yana da hannu a harin da aka kai a shinge sojoji na Zuma Rock kusa da Suleja, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar, tare da bayyana cewa ya taɓa aiki a ƙarƙashin wani babban jagoran ƙungiyar mai suna Abu Ikirimah wanda aka kama a 2024.” in ji majiyar kamar yadda NTA ta ruwaito.

Jami’an tsaro sun ce kama Yusuf wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin tabbatar da adalci ga waɗanda harin ya rutsa da su, da kuma kara tabbatar da yaki da ta’addanci a fadin Najeriya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Hukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8
X whatsapp