Home Labarai Yadda Lakurawa suka kashe masallata a Kebbi

Yadda Lakurawa suka kashe masallata a Kebbi

'Yan Ta'adda

Kamfanin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa aƙalla masallata biyar ne suka mutu yayin da wasu uku kuma suka jikkata a wani harin ramuwar gayya da mayaƙan Lakurawa suka kai a masallaci a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya, a daren Laraba.

Lakurawan sun buɗe wuta a masallacin dake ƙauyen Dadin Kowa a ƙaramar hukumar Maiyama yayin da masallata ke gudanar da sallar tarawihi a wata mai tsarki ta Ramadan.

Wani rahoton tsaro da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu ya ce an kashe mutane goma a harin.

Kakakin ‘yan sandan Kebbi, Bashir Usman, bai amsa buƙatar AFP na ƙarin bayani ba nan take, amma ya shaida wa NAN cewa harin ya biyo bayan kashe wasu daga cikin mayakan Lakurawa a wani “yunƙurin kautan ɓauna da bai yi nasara ba a kan jirgin soji.

Usman ya ce: “Harin na ramuwar gayya ne daga wasu yanbindiga da ake zargin ƴan kungiyar Lakurawa ne, bayan wani yunƙurin kautan ɓauna da bai yi nasara ba a kan rundunar sojin Najeriya.”

An danganta Lakurawa da kai hare-hare da dama a al’ummomin arewacin jihar Kebbi da jihar Sokoto dake makwabta.

Yan kungiyar na kai hare-hare daga sansanin su a cikin daji tare da satar dabbobi da kuma tilastawa mazauna biyan haraji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp