Home Labarai Hukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatanta

Hukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatanta

Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana ranar 13 ga Mayu, 2026 a matsayin ranar da za a fara jigilar rukunin farko na alhazan jihar zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Babban daraktan hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara ta aiki da ya kai majalisar dokokin Jihar Kano, bisa ga jadawalin jigilar alhazai da hukumar Alhazai ta Ƙasa ta fitar kamar yadda mai magana da yawun hukumar a Kano Sulaiman A Dederi ya sanar.

Ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan muhimman shirye-shirye da suka haɗa da tantance takardu,da tsare-tsaren jigila, da wayar da kai, da gwajin lafiya da kuma sauran matakan da suka dace domin tabbatar da an gudanar da aikin cikin tsari da kwanciyar hankali.

Alhaji Matawalle ya jaddada cewa yin bayani ga majalisar dokoki musamman Kwamitin Hajji kafin fara jigilar alhazai al’ada ce mai karfafa guiwa da kuma tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye suna tafiya yadda aka tsara.

Ya kuma tabbatar da cewa zai yi amfani da gogewarsa a harkokin Hajji tare da bullo da sabbin tsare-tsare domin tabbatar da cewa alhazan Kano sun gudanar da ibadarsu cikin sauƙi, tsaro da cikakken kulawa.

Da yake jawabi tun da farko, Mataimakin Kakakin majalisar dokokin Jihar Kano kuma mamba a Kwamitin Hajji, Hon. Muhammad Bello Butu-Butu, ya taya babban daraktan murnar nadin da aka yi masa, yana mai bayyana cewa nadin ya dace da ƙwarewarsa da jajircewarsa.

Ya kuma tabbatar da cewa Majalisar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Hukumar domin ganin an cimma burin gudanar da Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp