Home Taska Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Jihar Benue

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Jihar Benue

'Yan Ta'adda

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Jihar Benue

 

Aƙalla mutum 10 aka kashe da sanyin safiyar Laraba bayan wasu mahara ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen Saai da ke gundumar Mbajir a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

Mazauna yankin sun ce maharan sun kutsa cikin ƙauyen da tsakar dare, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin yankin na cewa wasu daga cikin mutanen sun jikkata sakamakon harbin bindiga, yayin da aka kashe wasu ciki har da Mchiaga Akaa Agbondo, wanda ya ce “an sassara shi da adda har ba a gane fuskarsa”.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da kula da wasu da suka jikkata a asibiti.

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma ya je yankin domin duba halin da ake ciki.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah wadai da harin, inda ya yi zargin cewa maharan ƴan ta’adda ne da ke fakewa da sunan makiyaya, domi kawo cikas ga ayyukan noma da samar da abinci a jihar.

Gwamnan ya umarci jami’an tsaro su tura ƙarin dakaru zuwa yankin Saai da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da yankin domin farautar waɗanda suka kai harin, tare da ƙara tsaurara matakan tsaro ga manoma.

Rundunar ƴansanda ba ta fitar da wata saarwa game da harin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Anambara: Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'addan IPOB/ESN, Sun Kwato MakamaiHukumar Kwastam ta Kano ta Mika Magungunan da ba a yi wa Rijista ba ga NAFDAC, ta Kuma yi Alƙawarin Tsaurara Matakan Aiki.Operation HADIN KAI: Harin Jiragen Sama Ya Kawar da 'Yan Ta'adda 36 a BornoFamadewa, Ribadu da Shirin Tsaron Kwanaki 90: Yadda YAShuaib ya Binciki Sanarwar OnanugaLabarin NIPSS Ya Bayyana Cin Zarafin Babban Jami'in Sojan Ruwa, Rear Admiral AA MustaphaƊaliban PRNigeria Sun Yaba da Gyare-Gyaren FRSC, Sun Nemi Ƙarin Ƙarfafa Sadarwa Kan Tsaron HanyaYadda Dalibai 4 Almajirai Suka Mutu Bayan Cin Kife da Ake Zargi da Guba a KanoSojoji Sun Ceto Mutane 14 da Aka Sace a Dajin KatsinaTinubu Ya Nada Abel Enitan A Matsayin Sabon Shugaban Ma'aikatan TarayyaRundunar Sojin Ruwan Najeriya ta Ceto Mutane 22 Daga Hannun Ƴan Fashin Teku Kimanin Malamai 200 ne Suka bar Jami'ar KASU - ASUUHukumar EFCC ta Gurfanar da Mutumin da ake Zargi da Damfarar Maniyyata Aikin HajjiKashi 40 Cikin 100 Kawai na Cibiyoyin Kiwon Lafiya a Duniya ke da Tsabta - MDDDakarun Sojin Najeriya Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa da Mutane a Zamfara
X whatsapp