Home Taska An Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban...

An Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban Jos

An Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban Jos

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gurfanar da mutum 24 a gaban kotun majistare bisa zarginsu da hannu a kisan wata matar aure da wasu fusatattun mutane suka yi a Maraban Jos.

Ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifukan bayar da gudummuwa wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama’a, lalata dukiyoyi, lalata kadarorin gwamnati da na ‘yan sanda, da kuma kisan kai.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ta jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar ta ce an gurfanar da su ne bayan binciken da ‘yan sanda suka gudanar kan lamarin da ya faru a ranar 21 ga Yunin 2026, lokacin da aka kashe matar “bayan mutanen sun ƙwace ta daga hannun ‘yan sanda.”

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga Yulin 2026, inda kotun ta bayar da umarnin a tsare dukkan waɗanda ake zargin a gidan yari har sai an kammala shari’ar.

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da binciken fiye da mutum 100 da ake zargin su da hannu a lamarin, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da laifi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp