An Kashe Matashi Kan Murfin Tayar Adaidaita Sahu a Kano
Wata Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi, Auwal Adam, a gidan gyaran hali bisa zargin hannu a kisan wani abokin sana’arsa bayan wata taƙaddama kan murfin tayar babur ɗin Adaidaita Sahu.
Mai Shari’a Sakina Aminu Yusuf ce ta bayar da umarnin tsare matashin bayan ’yan sanda sun gurfanar da shi bisa tuhume-tuhumen haɗa baki da kisan kai.
Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, matashin da ake zargin ya musanta aikata laifin.
Read Also:
Lauyan masu gabatar da ƙara, A.I. Buhari, ya roƙi kotun da ta ɗage shari’ar domin ba wa masu gabatar da ƙara damar neman shawarar shari’a daga gwamnati.
Alƙaliyar ta amince da buƙatar, inda ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga Satumba, 2026.
’Yan sanda sun yi zargin cewa Auwal Adam da wasu abokansa, waɗanda har yanzu ake nema ruwa a jallo, suna da hannu wajen kisan abokinsu, Aliyu Abubakar Badawa.
A cewar ‘yan sandan, lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakanin mutanen kan murfin da ake rufe tayar babur mai ƙafa uku na Adaidaita Sahu.










